Tarayyar Turai (EU) ta ware €557 miliyan domin taimakon jinƙai ga Najeriya da sauran ƙasashen Afirka a 2026, a cikin sabon kasafin €1.9 biliyan da ta sanar.
Yankunan da za su amfana sun haɗa da Arewacin Yammacin Najeriya, Sahel, Lake Chad Basin, Gabashin Afirka, da sauran manyan yankunan da ke fama da rikice-rikice.
EU ta ce ana yin wannan ne saboda yawancin mutane miliyan 239 na buƙatar gaggawar taimako yayin da gudunmawar ƙasashen duniya ke raguwa.
Kwamishinar EU Hadja Lahbib ta ce Turai na ƙara ƙoƙari domin tallafa wa abinda ake kira mummunar bukatar jinƙai. Ta kuma tabbatar da cewa EU za ta ci gaba da ba da abinci, magani, mafaka da kariya ga mutanen da ke cikin haɗari.
Baya ga Afirka, EU ta ware kuɗi domin Gaza da Gabas ta Tsakiya (€448m), Ukraine (€145m), Afghanistan da Pakistan (€126m), da sauran yankunan da ke fama da rikici.
Ta ce wannan ƙudiri kira ne ga haɗin guiwa, domin, “Turai na tashi tsaye wajen nuna goyon baya.”
