Gwamnatin Tarayya ta fara shirin haɗa manoma kanana miliyan 14 cikin harkar sarrafa rogo ta hanyar Cassava Bioethanol Value Chain Project.
Ministan Tsare-Tsare da Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya ce shirin zai iya taimaka wa Najeriya ta adana fiye da Naira tiriliyan 3 a shekara ta hanyar haɗa bioethanol da fetur (PMS), domin rage dogaro da shigo da mai daga waje.
Ya bayyana cewa za a inganta noman rogo da fasaha, kasuwa, da samar da kayan aiki, tare da amfani da samfurorin rogo kamar starch, CO2, da abincin dabbobi.
An gudanar da taron horaswar ne a Enugu domin karfafa gwaninta ga gwamnati, manoma, masana’antu, da jami’o’i.
Shirin na nufin habaka masana’antu, sauyin makamashi, da inganta rayuwar al’umman karkara.
