Hukumar Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da Babban Bankin Ci gaban Afirka (AfDB) sun fara babban taron tattaunawa kan tsawaita Takardar Dabarar Haɗin Kan Yankin Yammacin Afirka (2020–2027).
Taron, wanda zai gudana na tsawon kwanaki uku daga 4 zuwa 6 ga Fabrairu, 2026, ana gudanar da shi a Hedikwatar Hukumar ECOWAS da ke Abuja, tare da halartar manyan jami’an gudanarwa daga bangarorin biyu.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan tsare-tsaren jagoranci da dorewar Takardar Dabarar Haɗin Kan Yankin Yammacin Afirka, wadda ta ƙare a Disamba 2025.
A yayin bude taron, Darakta-Janar na AfDB a Yammacin Afirka, Mista Lamin Barrow, ya jaddada bukatar tsawaita wannan takarda domin tabbatar da dorewar shirye-shiryen yankin da ake aiwatarwa yanzu da kuma na gaba.
Ya ce, “Tsawaita wannan muhimmin tsari na shiryawa na yankin yana da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da ci gaban sabbin ayyuka a ƙarƙashin haɗin gwiwar Banki da ECOWAS.”
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Hukumar ECOWAS, Dr. Omar Alieu Touray, ya yaba wa Babban Bankin Ci gaban Afirka bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar.
Ya bayyana cewa goyon bayan AfDB ya shafi muhimman sektoci da dama ciki har da noma, ababen more rayuwa, kasuwanci, kwastam, gina ƙwarewa, lafiya, ilimi, masana’antu da makamashi.
Ana sa ran wannan tattaunawa za ta daidaita abubuwan da aka fi ba wa muhimmanci a haɗin kan yankin da sabbin ƙalubalen ci gaba, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ECOWAS da AfDB wajen inganta manufofin haɗa tattalin arzikin Yammacin Afirka.
