Masana da kwararrun ’yan bincike sun bukaci ƙasashen Afrika da su kalli cikin gida su kuma sake tsara kansu yadda ya dace domin ci gaba da zama masu tasiri a tsarin duniya mai sauyawa da sauri.
An yi wannan kira ne a ranar Alhamis a Legas, a wani taron bita na musamman da aka gudanar domin tunawa da cika shekaru 50 da kisan tsohon Shugaban Ƙasa na Najeriya, Janar Murtala Mohammed.
Taron, wanda aka yi ƙarƙashin taken “The Africa Coming of Age Dialogue Series,” ya samu haɗin guiwar Murtala Mohammed Foundation da Nigerian Institute of International Affairs (NIIA).
Ya tattaro masana manya, masu tsara manufofi da shugabannin tunani domin nazarin al’amuran siyasa, tattalin arziki da ci gaban ƙungiyoyi a Afrika, shekaru hamsin bayan sanarwar Murtala Mohammed cewa, “Afrika ta balaga.”
Yayin da yake jawabi a wajen taron, Darakta-Janar na NIIA, Farfesa Eghosa Osaghae, ya bayyana rashin iyakance ga tsarin duniya (globalisation) a matsayin babban abin da ke tauye kwarin gwiwa da himmar cigaban Afrika.
A cewarsa, ƙasashe da dama a Afrika sun yi dogaro sosai da hanyoyin waje maimakon gina ƙarfinsu daga cikin gida.
Ya ce, “Mun fara tunanin cewa mafita ba daga cikinmu za ta fito ba, sai daga waje; dole mu koyi yin imani da kanmu. Afrika cibiyar ƙarfi ce.”
Tsohon Ministan Harkokin Waje kuma fitaccen ɗan diflomasiyya, Farfesa Bolaji Akinyemi, ya yi tsokaci game da rayuwa da shugabancin marigayi Janar Murtala Mohammed, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai jarumta, ladabi, da tausayi wanda tasirin sa ya wuce lokacin mulkinsa na watanni bakwai.
Akinyemi ya kalubalanci shugabannin Najeriya na yanzu da su koyi darussa daga gadon Murtala Mohammed, musamman hangen nesa na Pan-Afrika, wanda ya ce wata makarantar tunani ce da ta kamata a zurfafa bincike akanta don farfado da ita.
Masu shirya taron sun bayyana cewa wannan tattaunawa ba wai tunawa kawai ba ce, amma dandali ne na tattaunawa mai dogaro da shaidu, haɗa juna tsakanin matasa da tsofaffi, da samar da ingantattun bayanai ga manufofi kan matsayin Afrika a tsarin duniya na yau.
