Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi gwamnonin jihohi a liyafar Iftar ta Ramadan a Fadar Shugaban Kasa, Abuja, domin ci gaba da al’adar cin abinci tare da shugabannin siyasa a cikin watan Ramadan.
An fara cin abincin Iftar da misalin ƙarfe 7:00 na yamma, kuma wannan shi ne karo na uku a jere da Shugaban ke tara gwamnonin ƙasar domin cin abinci tare a Aso Rock.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, sun halarci taron tare da ministocin tarayya da Sufeto Janar na yan Sanda, Kayode Egbetokun.
Gwamnan Jihar Imo kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, Hope Uzodinma, ya jagoranci sauran gwamnonin da suka halarta, ciki har da:
– Gwamnan Abia, Alex Otti
– Gwamnan Cross River, Bassey Otu
– Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
– Gwamnan Benue, Hyacinth Alia
– Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru
Sauran sun haɗa da:
Gwamnan Jigawa, Umar Namadi;
Gwamnan Kaduna, Uba Sani;
Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu;
Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang;
Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori;
Gwamnan Ekiti, Biodun Abayomi Oyebanji;
Gwamnan Edo, Monday Okpebholo.
Mataimakin Gwamnan Bauchi ma ya halarta.
A baya, Shugaba Tinubu kan yi amfani da tarukan Iftar domin ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya tsakanin jam’iyyu. Ana sa ran ƙarin tarukan Iftar za su gudana a Fadar Shugaban Kasa yayin da azumin Ramadan ke ci gaba.
