Gwamnatin Najeriya ta ce yarjejeniyar da aka kulla da Birtaniya tana tabbatar da tsaro, tsari, da doka a harkar hijira tsakanin kasashen biyu, tare da yaki da yin hijira ta barauniya.
Mai ba Shugaba shawara kan Labarai, Bayo Onanuga, ya ce ana yada bayanan da ba daidai ba. Ya jaddada cewa yarjejeniyar ba ta tilasta Najeriya ta karɓi ‘yan kasashen waje ba sai dai ’yan Najeriya da aka tabbatar da su aka amince a mayarwa.
Ya ce duk mutumin da za a mayar dole a tabbatar da sunansa sau da dama. Idan aka yi kuskure, Birtaniya za ta mayar da shi kuma ta biya kudin dawowarsa.
Yarjejeniyar ta kuma tanadi cewa:
A girmama hakkin ɗan adam ga duk wanda ake dawo da shi.
A ba su damar haɗa dukiyar su kafin su koma.
A ba su tallafin sake daidaitawa kamar masauki, sufuri, horo, da damar neman aiki ko kafa kasuwanci.
Nigeria Immigration Service ce kaɗai ke da ikon bayar da takardun tafiya.
Fadar Shugaban Kasa ta ce yarjejeniyar za ta gudana na shekaru biyar, kuma an yi makamanciyar yarjejeniya a baya.
