Hukumar NiDCOM ta sanar da shirye-shiryen gudanar da Najeriya Diaspora Economic Conference (NIDEC) 2026, babban taron masu zuba jari na duniya domin ƙarfafa gudunmawar ’yan Najeriya a ƙasashen waje ga cigaban tattalin arzikin ƙasa.
Shugabar NiDCOM, Dr Abike Dabiri-Erewa, ta ce taron zai gudana a 13–15 ga Agusta 2026 a Mississauga, Toronto, Canada, tare da taken “Invest Nigeria, Thrive Abroad.”
An zaɓi Canada ne saboda yawan ƙwararrun ’yan Najeriya da ke can, kuma taron zai haɗa su da damar zuba jari a gida. NIDEC zai mayar da hankali kan fannoni kamar fasaha, noma, makamashi, lafiya, gidaje da sabis na kuɗi.
Za a yi haɗin gwiwa da ofisoshin jakadanci domin sauƙaƙa shiga, tare da shirye-shiryen biki na al’adu da Flavours of Nigeria da Headies Awards.
Dr Dabiri ta kira ’yan kasuwa da ƙwararru su yi amfani da damar domin samun jari, haɗin gwiwa, da tallafa wa ci gaban Najeriya.
