Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), da ta Nijar sun gudanar da babban taron haɗin gwiwa a Abuja domin ƙarfafa tsaro, musayar bayanai, da sauƙaƙa zirga-zirgar kaya tsakanin ƙasashen biyu.
Shugaban Kwastam na Najeriya, Adewale Adeniyi, ya ce Najeriya za ta ci gaba da tallafa wa Nijar wajen motsa kayayyakin transit cikin sauri, tare da samar da “safe corridors” domin rage tsaiko. Ya gargadi ’yan kasuwa da ke kokarin karkatar da kaya cewa za a hukunta su.
Daraktan Kwastam na Nijar, Muhammadu Yaqouba, ya ce sun zo domin magance jinkirin manyan motoci da kuma matsalolin tsaro na yankin. Ya bayyana cewa Nijar ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’addanci tun 2024 ta hanyar Operation Saran Kasa.
Shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Najeriya, Janar Garba Laka, ya ce Najeriya da Nijar suna da tarihi da al’adu ɗaya, kuma bukatar haɗin kai ta ƙaru saboda barazanar makamai, miyagun ƙwayoyi da ’yan ta’adda.
An yi alkawarin ƙara haɗin kai domin inganta tsaro da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
