Guinea- Conakry New President
Shugaban juyin mulkin Guinea, Mamady Doumbouya, ya ci zaben shugaban kasa bisa sakamakon wucin gadi da aka fitar a ranar Talata, wanda ke nuna komawar kasar zuwa mulkin farar hula.
Doumbouya, tsohon kwamandan rundunar musamman wanda ya kifar da Alpha Condé a 2021, ya samu 86.72% na kuri’un zaben 28 ga Disamba. Kotun Koli na da kwanaki takwas don tantance sakamakon idan an samu koke-koke.
Fitattun yan adawa kamar Condé da Cellou Dalein Diallo suna gudun hijira, wanda ya bar Doumbouya tare da hamayya mai rauni.
Kodayake kundin tsarin mulkin farko ya hana shugabannin juyin mulki takara, sabon kundin tsarin mulkin da aka kada kuri’a a Satumba ya cire wannan hani.
Hukumar zabe ta ce an yi 80.95% turnout, duk da cewa alamu sun nuna rashin fitowar jama’a sosai a Conakry.
Guinea na da manyan ma’adanan bauxite da Simandou, tudu mafi arzikin ƙarfen ƙarfe da ba a fara hakowa ba, wanda Doumbouya ke cewa gwamnatinsa ta dage wajen farfado da shi.
Gwamnatinsa ta kuma kwace lasisin Guinea Alumina Corporation daga reshen Emirates Global Aluminium a bana.
