Kwamitin Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Manyan Asibitoci ya gabatar da Lambar Yabo ta Kwarewa (Award of Excellence) ga tsohon Daraktan Kiwon Lafiya na Asibitin Kula da Cututtukan Kwakwalwa na Tarayya (FNPH) Kware, Jihar Sokoto, Farfesa Shehu Sale, bisa kyakkyawan aikinsa.
Farfesa Sale, kwararren likitan cututtukan kwakwalwa, shi ne tsohon Daraktan Kiwon Lafiya na FNPH Kware, kuma an ba shi wannan lambar yabo ne domin gagarumar jagoranci da kuma hanzarta bunƙasa asibitin daga shekarar 2017 zuwa 2025.
An mika lambar yabon ne ta hannun Babban Daraktan Kiwon Lafiya (CMD) na Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) Kano, Farfesa Abdulrahaman Sheshe, a ranar Asabar a Sokoto.
Sheshe ya yaba wa Sale bisa sauya FNPH zuwa ingantaccen asibiti na zamani da ke bayar da ƙwararrun ayyukan kula da lafiyar kwakwalwa da sauran ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.
Haka kuma, Babban Daraktan Kiwon Lafiya na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodio (UDUTH) Sokoto, Farfesa Anas Sabir, ya yabawa Sale kan jajircewarsa da basirar jagoranci.
Taron ya samu halartar sababbin Daraktan Kiwon Lafiya na FNPH Kware, Dr. Abubakar Baguda Sulaiman, da sauran manyan baki.
