Najeriya da Jamhuriyar Benin sun sabunta dangantakarsu tare da shirya zurfafa haɗin gwiwa a diflomasiyya, tsaro da tattalin arziki, yayin wata ganawa ta manyan jami’an ƙasashen biyu a Abuja.
A taron, jami’an Benin sun yabawa Najeriya bisa goyon bayan da ta bayar, suna bayyana ta a matsayin makwabciya mai muhimmanci ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yammacin Afirka.
Najeriya ta tabbatar da ƙudurin ta na ci gaba da haɗin gwiwa da Benin, tana mai jaddada cewa duk abin da ya shafi Benin, yana shafar Najeriya.
