Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da Kwamitin WorldSkills Nigeria domin inganta hazakar matasa da kuma kara musu gasa a matakin duniya.
Ministan Ilimi, Dr. Maruf Alausa, wanda ya kaddamar da kwamitin a Abuja, ya ce wannan mataki zai tabbatar da cewa ƙwarewar da matasa ke samu a Najeriya ta yi daidai da ka’idojin duniya.
WorldSkills Nigeria na aiki tare da WorldSkills International wajen bunkasa fasaha, ƙwarewa, da horon sana’o’i (TVET) domin haɓaka masana’antu da tattalin arziki.
Alausa ya ce kafa kwamitin na nufin gina ƙwararrun matasa da za su iya fafatawa a ko’ina a duniya, tare da karfafa sha’awar sana’o’i a matsayin muhimmin matakin karatu.
An bayyana cewa Najeriya ta shiga WorldSkills International a 2024 bayan shafe fiye da shekaru goma tana ƙoƙari da haɗin gwiwar NBTE da sauran hukumomi.
Shugabannin NBTE da WorldSkills Nigeria sun yaba da matakin, suna mai cewa zai ƙarfafa haɗin kan masana’antu da cibiyoyin koyon sana’a, tare da gina tattalin arzikin da ya dogara da ƙwarewa.
