Masar ta tabbatar da goyon bayanta ga Rundunar MNJTF yayin da ake ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a yankin Tafkin Chadi. Jakadan ƙasar a Chadi, Ambassador Tarek Youssef, tare da Atashen Tsaro, Staff Colonel Ahmed Gamal El-Barbary, sun kai ziyara hedikwatar MNJTF domin bayyana wannan ƙudiri.
A wata sanarwa, MNJTF ta ce Jakadan Masar ya yaba da rawar rundunar wajen yaƙi da ta’addanci, tare da nuna sha’awar ƙara fahimtar tsarin aikin rundunar.
Atashen Tsaro ya ce Masar na son haɗin kai a fannonin horaswa, tallafin kayan aiki da ayyukan tsaro.
Kwamandan MNJTF, Major General Saidu Tanko Audu, ya gode wa Masar bisa wannan goyon baya, yana mai jaddada nasarorin rundunar wajen raunana Boko Haram da dawo da ‘yan gudun hijira. Ya kuma yi kira ga ƙarin haɗin kai musamman a bayanan sirri, rigakafin bama-bamai, da fasahar dakile jiragen sama marasa matuki.
