Bankin Duniya ya amince da ƙarin kuɗaɗe don ci gaba da aiwatar da shirin SPESSE, wanda ke horar da ƙwararru a fannin sayen kaya, kare muhalli da ka’idojin zamantakewa a Najeriya.
Rahoton Bankin ya nuna cewa aikin ya yi kyakkyawan ci gaba, inda aka cimma duk manyan manufofin da aka sa masa. Shirin, wanda Gwamnatin Najeriya, Bankin Duniya da Hukumar Kula da Jami’o’i (NUC) ke tallafawa, ya taimaka wajen rage ƙarancin ƙwararru a bangarorin gwamnati da masu zaman kansu.
An horas da fiye da mutane 85,000, yayin da 3,429 suka yi nasarar samun takardar shaidar ƙwarewa a shekarar 2025. Hakan ya sa Bankin Duniya ya tsawaita shirin zuwa Yuni 2026.
Hukumar Kula da Sayen Kaya ta Ƙasa (BPP) ta bayyana shirin sanya karatun SPESSE ya zama tilas ga dukkan jami’an procurement. Manufar ita ce inganta gaskiya, inganci da shugabanci nagari a tsarin sayen kaya na Najeriya.
